Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaro A Amurka Sun Kama Wani Mutum Dake Shirin Sumogan Dabbobi

Wani jami'in tsaro a wata tashar jiragen saman Amurka yake duba takardun wata fasinja.

A jiya Talata, hukumar kula da matakan tsaron ababen hawa tace an gano dabbobin ne a lokacinda mutumin yabi ta nau’rar cajin jikin mutum, a filin saukar jiragen sama ta kasa da kasa a birnin Miami jihar Florida a makon jiya.

An kama wani mutum a lokacinda yayi kokarin yin somagal din wani jinsi maciji da kunkuru, daya boye cikin wandonsa yana kokarin shiga wani jirgin sama.

A jiya Talata, hukumar kula da matakan tsaron ababen hawa tace an gano dabbobin ne a lokacinda mutumin yabi ta nau’rar cajin jikin mutum, a filin saukar jiragen sama ta kasa da kasa a birnin Miami jihar Florida a makon jiya.

Shi dai wannan mutumin yasa macijin da kunkuru cikin wata jakar leda sa’anan ya boye a cikin wandonsa.

Hukumomi basu baiyana suna mutumin ba, amma yana kokari ne yaje kasar Brazil. An dai kama shi a saboda ya keta dokokin yin smogal din dabbobi.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG