Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Arziki Ya Ragu A Amurka


Shugaban babban bankin Amurka, Ben Bernanke
Shugaban babban bankin Amurka, Ben Bernanke

Rahoton babban bankin Amurka ya ce faduwar darajar gidaje na cikin dalilan raguwar arzikin

Sabbin bayanai sun nuna cewa matsalar tattalin arziki ta yi matukar rage arziki a gidajen Amurka, wanda hakan ya taimaka wajen tsananta matsalar, da kawo jan kafa wajen farfadowa kuma hakan ya jigata masu mtsakaicin karfi.

Rahoton wanda babban bankin Amurka ya gabatar, ya ce abun da ya kara raunana al’amarin shi ne faduwar darajar gidaje tsakanin shekarar 2007 da 2010.

Babban masanin ilimin tattalin arzikin da ke tare da kungiyar kamfanonin masu saida gidaje a Amurka, Lawrence Yun, ya ce faduwar darajar gidaje ta sa iyalai yin tsumulmula da kudaden su, wanda hakan ya haifar da raguwar bukatun mabukata a kasa kuma ya dakushe bunkasar tattalin arziki.

Rahoton ya ce farashin gidaje ya taimaka wajen zaftare arzikin masu matsakaicin karfi daga dola dubu 126 zuwa dola dubu 77 a tsawon shekaru fiye da uku.

XS
SM
MD
LG