Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Asusun tallafi na Bill da Milinda Gates ya kashe dala miliyan 6.7 a jihar Gombe


Bill Gates da matan shi Melinda Gates

Asusun tallafi na Bill da Melinda Gates ya kashe dala miliyan shida da dubu dari bakwai karkashin shirin “Society for Family Health”

Asusun tallafi na Bill da Melinda Gates ya kashe dala miliyan shida da dubu dari bakwai karkashin shirin kula da lafiyar mata da ake kira “Society for Family Health” yayin gudanar da wani aiki na tsawon shekaru biyu da aka gudanar a kananan hukumomi 11 na jihar da nufin ceton rayukan mata da kananan yara dubu sittin daga cututukan da suka jibinci daukar ciki.

Jami’in gudanar da ayyuka na shirin kula da lafiyar kananan yara da asusun Bill da Milinda Gates ya dauki nauyi, Mr Saul Morris, ya bayyana cewa, mata 248 wadanda suka mika kai domin tallafawa al’umma, da kungiyar hadin kan mata Musulmi ta Najeriya (FOMWAN) ta horas domin bada shawarwari ga mata kan yadda zasu kula da kansu da kuma jariransu kafin daukar ciki da kuma bayan haihuwa.

Da yake jawabi a wajen wani taron manema labarai a karshen shirin makon jiya, Mr Bright Ekweremadu, manajin darektan cibiyar Society for family Health, ya bayyana cewa, gudanar da shirin ya zama dole lokacin da binciken kiwon lafiya na kasa da aka gudanar a shekara ta 2008 ya nuna cewa kashi 17% na mata masu juna biyu ne suke kai ga haihuwa a a asibiti a jihar Gombe.

Bisa ga cewarshi, wannan ya nuna akasarin mata masu ciki suna haihuwa ne ba tare da tallafin kwararru ba. Abinda yasa ake samun matsaloli da yake kai da rasa rayukan iyayen da kuma jariransu.

Shirin ya kuma sami goyon bayan kimanin direbobi 695 membobin kungiyar ma’aikatar sufuri ta kasa (NURTW) wadanda suka bada gudummuwar motocinsu domin daukar mata da jariran da suke bukatar kulawa ta gaggawa. Shirin ya kuma yi aiki da masu kemis 760 wajen samar da kayan karbar haihuwa masu tsabta, yayinda aka horas da unguwarzoma 315 kan yadda zasu karbi haihuwa cikin tsabta da kuma sanin lokacin da mace take cikin hadari su tura ta asibiti cikin gaggawa.

An kaddamar da shirin ne da ake kira “Inganta Rayuwar Iyali,” da aka gudanar na tsawon shekaru biyu a watan Nuwamba 2009 da nufin rage cututuka da mace mace tsakanin mata masu juna biyu ta wajen daukar matakai dabam dabam. Aka kuma kamala ranar 8 ga watgan Maris 2012.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG