Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Asusun tallafi na Bill da Milinda Gates zai tallafa wajen aiwatar da wani sabon salon rigakafin shan inna


Bill da Melinda Gates
Bill da Melinda Gates

Rashin kasancewar kananan yara a gida lokacin rigakafin shan inna ke gurguntar da nasarar shirin

Rashin kasancewar kananan yara a gida lokacin rigakafin shan inna ke gurguntar da nasarar shirin.

Bincike na nuni da cewa, rashin kasancewar kananan yara a gida ko kuma boye su da iyaye ke yi a lokacin rigakafi shine sanadin gaza yiwa kashi 83% allurar rigakafi a Najeriya.

Ta dalilin haka wadansu gwamnatocin jihohin arewacin kasar da suka hada da Kano da kuma Jebbi suka aiwatar da wani shirin na amfani da ma’aikatan sa kai daga cikin al’umma wajen gudanar da ayyukan rigakafi da kuma wayar da kan al’umma kan harkokin lafiya.

Jihar Kano ta horas da masu aikin sa kai 557 wadanda daga ciki 388 suke gudanar da aikin tsakanin al’umma yayinda jihar Kebbi kuma ta horas da masu aikin sa kai 200.

Babban jami’in rigakafin shan inna na asusun tallafawa kananan yara UNICEF a Najeriya, Tommi Laulajainen yace an fi samun kalulaba a jihar Kano wajen aiwatar da wannan shirin, sabili da yawan kauyukan da ake bukatar yiwa kananan yara allurar rigakafi.

Shirin da ake gudanarwa tare da tallafin asusun Bill da Milinda Gates da kuma cibiyar yaki da cututuka ta kasa CDC, zai maida hankali wajen yiwa kanannan yaran da basu sami rigakafi ba allurar a rukunin rigakafin na uku, musamman a jihohin Zamfara, Jigawa, Katsina, Yobe da kuma Borno.

Za a dauki ma’aikatan sa kai dubu biyu da dari da hamsin wadanda za a tura kauyukan da ake da kananan yaran da basu sami rigakafi ba.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG