Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Atiku Abubakar Na Ganin Dimokradiya Na cikin Hadari a Najeriya


Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya
Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya

Yayin da yake mayar da martani dangane da tsige gwamnan Adamawa tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar yacelamarin ya jefa dimokradiya cikin wani hadari a Najeriya

Ana cigaba da cecekuce game da tsige gwamnan Adamawa Murtala Nyako da majalisar tayi kwana kwanan nan.

A wata sanarwar da ya fitar tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar yace tsige gwamnan yasa yana ganin dimokradiyar kasar cikin hadari.

Alhaji Garba Shehu kakakin Atiku Abubakar yace abun da Atiku Abubakar ke cewa shi ne lamarin bai yi masa dadi ba kuma yana ganin akwai abubuwa da yawa da aka yi akan batun da suka saba ka'ida da kuma suka saba cancanta da kamala domin magana ce ta dimokradiya. Idan Allah Ya baka iko kada kayi anfani da ikon ka gallazawa wani. Su kansu 'yan majalisa da aka yi anfani da su aka aiwatar da tsigewar su yi hankali domin wadanda suka yi anfani dasu ba mutane ne masu rike amana ba.

A bangaren mukaddashin gwamnan jihar Ahmadu Umaru Sintiri sun mayar da martani. Stephen Maduwa mai ba mukaddashin gwamnan shawara akan harkokin yada labarai yace yakamata Atiku Abubakar ya sani cewa ba shugaban kasa ba ne ya cire Murtala Nyako ba. 'Yan majalisar Adamawa suka yi kuma mutane ne masu ilimi da basira. Yace a tuna a 2008 an yi kokarin tsige Murtala Nyako. Dangane da gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso, yace me yasa ya yiwa mutanen Kano aiki. Yayi gidaje, yayi hanyoyi koina a Kano da wasu abubuwa. A Adamawa shin menene Murtala Nyako yayi. Shin shugaban kasa ne yasa Kwankwaso yayi abubuwan da yayi. Shin shugaban kasa ne ya hana Nyako biyan albashin ma'aikata.

Yanzu sojoji na cikin shirin ko ta kwana a jihar yayin da talakawa ke cigaba da bayyana ra'ayoyin da suke karo da juna.

Mukaddashin gwamnan ya nada wasu sabbin mukarraban gwamnati. Ya nada Farfasa Liman Tukur a matsayin sabon sakataren gwamnati kana kuma yayi alkawarin biyan ma'aikata hakkokinsu.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz

XS
SM
MD
LG