Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Atiku, Buhari Sun Yi Hasashen Samun Nasara


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Hagu) da dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar (Dama)

Yanzu haka ana ci gaba da kidayar kuri'un da aka jefa a ranar Asabar a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun a Najeriya.

'Yan Najeriya sun ci gaba da jiran sakamakon zabe tun daga jiya Lahadi yayin da aka ci gaba da kidayar kuri’un zaben shugaban kasar, inda 'yan takara suka yi matukar fafatawa.

An ci gaba da yin zaben a gurare kadan a wasu yankuna, sannan hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta (wato INEC a takaice) ta ce za ta sake saka ranakun da za’a sake zabe a wasu bangarorin jihohin Legas, Rivers da kuma Anambra, inda aka samu matsalolin jefa kuri’a a ranar Asabar.

Ba a bayyana hakikanin wuraren da abin ya shafa ba.

Wakilin Muryar Amurka, na sashen English to Africa, Peter Clottey, da ke Abuja, ya rawaito cewa hukumar zabe ta INEC, ta tsayar da yau Litinin a matsayin ranar da za ta fara bayyana sakamakon zaben.

Tuni Shugaba mai ci Muhammadu Buhari, da Babban abokin adawarsa Atiku Abubakar, kowannensu ya fara hasashen samun nasara.

Wani hadimin shugaba Buhari, Bashir Ahmad, ya aika da sakon Twitter a jiya Lahadi da safe yana cewa "ina kwananku ‘yan Najeriya, wannan karon ma godiya gare ku da kuka sake zabar shugaba Muhammadu Buhari jiya Asabar.

Tuni sakamako ya fara fitowa, kuma sun nuna an yi galaba matuka. Mafiya yawan masu kada kuri'a sun zabi Buhari, shugaba Muhammadu Buhari kuma ya kama hanyar nasara."

Abubakar na jam’iyyar PDP ya ce, su na samun nasara a wurare da dama, ciki har da birnin Legas, kuma Abubakar ya fitar da wata sanarwa yana cewa “saura kadan mu fita daga kangi da muka shiga na shekaru 4 ya zo karshe don haka tare za mu yi aiki domin ciyar da kasarmu gaba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG