Accessibility links

Yayin da ake samun takaddama tsakanin bangarorin APC a jihar Adamawa, gwamnan jihar Sanata Muhammadu Bindow Jibrilla, ya ce shi bai da uban-gida; kuma da Atiku da Nyako duk iyayensa ne

Rikicin bangaranci a jam’iyyar APC shiyyar jihar Adamawa tsakanin bangaren Atiku da tsohon gwamna Murtala Nyako ya dau wani sabon salo, ta yadda har sai da gwamna Muhammadu Bindow Jibrilla ya fito karara ya nuna ya na tare da dukkannin bangarorin biyu. Ya ce sam ba gaskiya ba ne cewa ya koma bangaren Atiku.

Wakilinmu a Adamawa Ibrahim Abdul’aziz ya ruwaito gwamna Jibrilla na cewa, “Wallahi Nyako uba na ne; kuma Atiku uba na ne; kuma ba mu da matsala a APC. Ka san sha’anin mutane; kowa na fadin abin da ya ga dama ne.” Gwamna Bindow, wanda ke amsa tambayar manema labarai, y ace fa sam bai da uban gida

Game da dangantakarsa da ‘yan Majalisar Dokokin jihar kuwa, gwamna Bindow ya ce a matsayin shi na tsohon dan Majalisar Dattijan Najeriya, ya san hakkin ‘yan Majalisa don haka zai bas u hakkokinsu. Sakateren Tsare –tsaren jam’iyyar ta APC a jihar ta Adamawa, Alhaji Ahmed Lawal y ace fadawan gidajen Atiku da Nyako ne ba su son a shirya.

XS
SM
MD
LG