A yau ne ake sa ran shugaban ma’aikatar shara’a na Amurka kuma attorney Janar, Jeff Sessions zai bayyana a gaban ‘yan Majalisar Dattawan Amurka kan rawar da ya taka a binciken da ake gudanarwa kan shisshisgin Rasha a harkar zaben shugaban kasar Amurka da aka yi bara.
Haka kuma ana sa ran zai sha tambayoyi kan ko yana da hannu a korar shugaban hukumar binciken FBI da aka yi James Comey.
Zaman da kwamitin binciken sirri na majalissar dokokin zai yi yau shine mataki na baya-baya akan bincike-binciken da ake yi game da katsalandan din Rasha a zaben shugaban kasa da aka yi shekarar da ta gabata.
Sessions ya janye jikinsa daga binciken hukumar FBI a watan Maris bayan da ya fadi cewa ya gana da Jakadan Rasha Sergei Kislyak har sau biyu ‘yan watanni kafin zaben da aka yi a watan Nuwamba.
Wannan ya sabawa da bayanin da ya bayar lokacin da ake kokarin tabbatar da shi akan mukamin na shi a watan Janairun wannan shekara, lokacin da ya ce bai taba saduwa da kowane irin jami’i na Rasha ba.
Facebook Forum