Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Ya Ce “Ban Ce Zan Rantse Ba Fa” Game Da Batun FBI


Trump da Comey
Trump da Comey

Shughaba Donald Trump ya bayana cewa akwai abubuwa da dama da James Comey ya fadi da ba gaskiya bane

Jiya Jumu’a ‘yan jaridu sun tambayi shugaban Amurka Donald Trump idan ko a shirye yake ya dauki rantsuwa dangane da shedar da tsohon shugaban hukumar binciken manyan laifukka ta Amurka ta FBI James Comey ya bayar gameda zancen da yace sunyi da shugaban, inda Trump ya bada amsar cewa “100 bisa 100 zan bada bayanin” amma kuma sai yayi sauri ya kara da cewa “ban ce zan rantse ba fa.”

Duk da haka Trump yace a shirye yake ya amsa duk wasu tambayoyin da zasu fito daga Robert Mueller, wanda shima wani tsohon shugaban hukumar ta FBI din ne, wanda kuma yanzu shine aka nada a matsayin shugaban hukumar gudanarda bincike mai zaman kanta da zata bi diddidigin gano ko Rasha ta taka wata rawa a cikin zaben shugaban kasan da aka yi bara a Amurka.

Da yake amsa tambayoyin ‘yan jaridu yayinda yake tarbon shugaban kasar Romania, Klaus Johannis jiya a fadar White House, shugaba Trump yace James Comey ya tabattarda gaskiyar abubuwa da yawa da shi Trump ya dade yana fada, koda yake kuma Trump ya kara da cewa “akwai abubuwa da yawa da Comey ya fada da ba gaskiya bane.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG