Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aung San Suu Kyi Tace Ana Baza Labarin Karya Game Da Kasar Ta


Aung San Suu Kyi
Aung San Suu Kyi

Shugaba Myanmar,Aung San Suu Kyi tace jamaa na kara gishiri cikin labarin tashe-tashen hankulan dake faruwa a kasar ta.

Shugabar kasar Myanmar, Aung san Suu Kyi tace ana warwatsa gagarumar jita-jita maras tushe akan tashin hankalin dake wakkana a jihar Rakhine ta kasarta, wanda ya tilasta wa Musulmi ‘yan jinsin Rohingya su kamar 125,000 yin gudun hijira zuwa kasar Bangladesh dake makwaptaka da tasu kasar.

A cikin wata sanarwa da ofishinta ya buga a kan dandalin Facebook, shugabar, wacce aka taba baiwa lambar karimci da yabawa ta Nobel tace ta zanta da shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, kan lamarin jiya Laraba, inda tayi mishi bayani gameda wasu hotunan da mukadashin frayim-ministan kasar tashi ya warwatsa a duniyar gizo na gawwawakin ‘yan Rohingya din, da tace basa ma da wata alaka da rikicin dake addabar kasar a yanzu.

Tace ta gaya wa shugaban na Turkiyya cewa irin wannan jita-jitar da ake bazawa na kara karfafa gwiwar abinda ta kira “’yan ta’adda”, kalimar da take yawan anfani da ita in tana maganar ‘yan-tawayen Rohingya da akace farmakin da suka kai akan wani barikin ma’aikatan tsaro shine ya janyo duk wannan rikicin dsake gudana a yanzu.

Sai dai kuma kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International ta la’anci wadanan magangannun na Aung San Suu Kyi, abinda kungiyar tace kalaman “rashin Imani ne.”

Tirana Hassan, Jami’ar maida Martani ta kungiyar Amnesty tace maimakon shugabar ta Myanmar ta nuna alhini kan abinda ke faruwa ga wadanan mutanen, sai ga shi tana son ta nuna kamar ba wani babban al’amari bane.

Mutane akalla 400 aka kashe tun daga lokacinda wata kungiyar ‘yantawayen Rohingya ta kai hare-hare akan ma’aikatun ‘yansandan jihar Rakhine, mazaunin aksarin ‘yan jinsin na Rohingya, abinda yassa daga baya su kuma ‘yansanda suka fito suka yi ta fattakar kauyukkan mutanen.

Facebook Forum

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG