Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ayyukan Da Gwamnatin Tarayya Ta Ki Kammalawa Sun Zarta Na Kudi Triliyan 5


Yanzu haka dai yawan aiyukan gwamnatin Najeriya da aka kasa kammalawa a fadin kasar sun haura na zunzurutun kudi Naira Trilion 15.

A yayinda yawan aiyukan bisa kididdigar hukumar kididdiga ta kasa ya haura dubu 12, koda yake jami'an ma'aikatar aiyukan kasar sunki cewa komai game da wannan matsalar.

Baya ga barazana ga harkokin tsaro, manya manyan gine-ginen gwamnati da aka yi watsi dasu a jihohi da daman a fadin kasar, asarar Miliyoyin kudi, su dai wadannan gine-ginen gwamnatin tarayya ko jihohi ko kananan hukumomi sun zarta na kudi Tiriliyan biyar a sassa daban daban na kasar.

Daya daga cikin aiyukan gwamnatin tarayya da ya yi kaurin suna amma ba a kammala shi ba shine kamfanin sarrafa karafa na kasa dake garin Ajakuta, a jihar Kogi, kamfanin da ba da dadewa ba gwamnati ta kafa masa kantoma na musamman da zai kula da ayyukan sa a shirye shiryen da gwamnatin ke yin a kokarin kwace shi daga hannun ‘yan kasuwa.

Ko mai ke haifar da matsalar rashin kammala ayyuka na gwamnatin Najeriya? Tambaya da wakilin sashen hausa na muryar Amurka Babangida Jibrin ya yiwa Injiniya Abubakar Haruna, na kamfanin ZBC dake jihar Kebbi, wanda ya alakanta lamarin da siyasa da rashin isassun kudi.

Da yake tsokaci akan illar dake tattare da rashin kammala irin wadannan ayyuka, Dr Dauda Muhammed, masanin tattalin arziki dake jami’ar Bayero ta Kano, ya bayyana cewa akwai illoli da dama, kama daga wargaza shirye shiren gwamnati na kasafin kudi zuwa kawo tsaiko ga cigaban al’umma.

wakilinmu a Legas Babangida Jibrin ya aiko mana da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG