Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ayyukan Karfi Na Illa Ga Rayuwar Yara - Inji Hukumar ILO


Hukumar kwadago ta duniya da ake kira ILO a takaice ta yi kira akan a kawar da ayyukan karfi na yarai, wanda ke jefa miliyoyin yara cikin kunci a sassan duniya daban-dabam.

Yara ‘yan shekaru 5 na cikin yara miliyan 152 dake aikin karfi. Galibinsu su na aiki na lokaci mai tsawo, kuma ana biyansu kudi kalilan wani lokacin ma ba a biyan su, kuma suna cikin yanayin wulakanci da wani abu mai kama da bauta. Hukumar ta ILO ta bada rahoton cewa kusan rabin yaran na yin munanan ayyukan karfi, dake barazana ga lafiyarsu ko su sa su cikin wani mummunan yanayi.

Hukumar ta ce yawanci ayyukan da suke yi su na fannin noma. Wasu wuraren da irin wadannan ayyukan ke tattare da barazana sun hada da fannin hakar ma’adinai, gine-gine, kamun kifi da kuma ayyukan gida. Beate Andrees, ita ce shugabar kare hakkokin jama’a a hukumar ta ILO.

Ta fadawa Muryar Amurka cewa yaran dake ayyukan karfi da suka fi muni, kamar saboda rashin biyan bashi da karuwanci, lafiyar jikin su da lafiyar kwakwalwar su na fuskantar matsalar da ba za ‘a iya magan cewa ba.

Shugabar ta ce bisa ga ka’idodin hukumar ta ILO, munanan ayyukan yara sun hada da ayyukan da zasu iya kawo tsaiko a girman yaro, har ma da yanayin sanin ya kamatan sa. Sun kuma hada da ayyukan tilas ko safarar yara da kuma sanya yaran ayyukan soja.

Ms. Andrees ta ce an sami ci gaba wajen rage sanya yara ayyukan karfi a nahiyar Asiya da yankin Latin na Amurka, amma kawar da wadannan ayyukan a Afrika na karuwa. Ta ce Afrika yanzu ta fi yawan yaran dake ayyukan karfi a duniya.

“Ba lallai wannan na nufin don ba a daukar mataki ba ne, amma kuma yana da alaka da yawan al’umma, da kaurar jama’a, da canjin yanayi, da kuma matsalolin tattalin arziki, wadanda ke taka rawa ta hanyoyi daban-dabam a sassa daban-dabam.” A cewar Ms Andrees.

Duk da wannan matsalar mai tada hankali, Andrees ta ce ta ji dadin ganin yadda kungiyar hadin kan Afrika ta AU ke daukar kwararan matakai don magance matsalar.

Ta kuma lura cewa kungiyar ta AU na hada wani shiri na tsawon shekaru 10 wanda zai gaggauta kawar da ayyukan karfi na yara, wanda ya je daidai da muradan Majalisar Dinkin Duniya da ake kira SDG a takaice.

Muradan na Majalisar Dinkin Duniya sun bukaci a kawar da ayyukan karfi na yara nan da shekarar 2025. Ko da yake, idan aka ci gaba da tafiya a yadda ake yi yanzu wajen rage ayyukan na yara, Andrees ta yi gargadin cewa haka ba za ta cimma ruwa ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG