Accessibility links

Azbinawa 'yan tawayen kasar Mali sun ayyana yancin cin gashi kai

  • Jummai Ali

Wasu 'yan gudun hijirar Mali da aka dauki hotonsu a wata Fabrairu a sansanin 'yan gudun hijirar Chinegodar a yammacin Niger,kusa da kan iyakar kasar Mali.

Juma'an nan Azibinawa ya tawayen kasar Mali suka ayyana samun 'yanci kuma sun bukaci sauran kasashen duniya da su amince da kafuwar sabuwar kasar su ta Azawad.

Azbinawa yan tawayen kasar Mali sun ayyana samun yanci a yau Juma'a, kuma sun bukaci sauran kasashen duniya da su amince da sabuwar kasar Azawad da suka kafa.

A wata sanarwar da suka sa a dandalin yanar gizon su, yan tawayen kungiyar yantar da Azawad da ake cewa National Movement for the Liberation of Azawad da turanci ko MNLA a takaice sunce zasu mutunta kan iyakokinsu da sauran kasashe.

Jiya Alhamis kungiyar MNLA ta ayyana tsagaita bude wuta tana mai fadin cewa ta cimma burinta.

Yan tawayen Azibinawan wanda suka fafata kafada da kafada da wasu mayakan Musulmi cikin kwanaki uku suka kwace ko mamaye biranen Kidal da Gao da kuma Timbuktu.

Ba'a dai tantance ba dada ko kungiyar 'yan yakin sa kai ta Ansar Dine wadda ta fafata tare da yan tawayen zata ajiye makamanta ko kuma a'a. Ita wannan kungiya wadda aka danganta da reshen kungiyar Al Qaida a arewacin Afrika da ake cewa AQIM a takaice ta kaddamar da amfani da shari'ar Musulunci a wasu yankuna.

Jiya Alhamis Ministan harkokin wajen Faransa Alain Juppe yayi kashedin cewa hanyar kawai da za'a bi na magance batun yan tawaye shine ta hanyar tattaunawa ba da karfin soja ba.

A yayinda haka ke faruwa kuma, ana ci gaba da matsawa sojojin Mali wadanda suka kwace mulki daga hannun shugaba Amadou Toumani Toure lamba. Sojojin dai sun zargi tsohon shugaban da laifin kasa baiwa sojoji kayayyaki da makaman da suke bukata domin yaki da yan tawaye.

XS
SM
MD
LG