Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba a Samun Raguwar Cutar Kanjamau Cikin Sauri a Nigeriya


Wasu mutane a harabar dakin taron kasa da kasa akan kanjamau

Alkaluma sun nuna cewa ba a samun raguwar masu fama da cutar kanjamau sosai a Najeriya.

Alkaluma sun nuna cewa ba a samun raguwar masu fama da cutar kanjamau sosai a Najeriya. A cikin rahoton da aka sawa suna “ruhoton cigaba na 2013 akan shirin duniya na maganin sabuwar kamuwa da kwayar cutar HIV a tsakanin yara zuwa 2015 da kuma tsare rayukan iyayensu mata” ne aka yi wanan bayanin. Bisa ga rahoton, Najeriya tana baya kasashe biyar – Lesotho, kasar Congo, Cote d’Ivoire, Chad da Angola - dukansu kasashe masu raguwa kadan ta cutar HIV ne.

Bisa ga bayanin da aka samo daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), da Asusun Tallafawa Kananan Yara (UNICEF), da kuma Cibiyar Kula da Yawan Al’umma ta Majalisar Dinkin Duniya UNFPA da kuma Bankin Duniya, ruhoton ya nuna cewa kamuwar yara ta HIV ta ragu zuwa kashi 8% daga 65,000 a 2009 zuwa 60,000 a 2012.

Haka kuma, daya daga 10, ko kashi 12 (260,000) na yara ne da suka kamu da HIV, suke samun maganin rigakafi a 2012, idan an kwatanta da kashi 8 na 2009. Sakamakon wannan ruhoton ya nuna cewa yawan mata wadanda suke shekarun haihuwa (15-49) da suke kamuwa da HIV bai canza ba sosai tun 2009. Adadin ya ragu kadan a cikin shekaru hudu daga 120,000 zuwa 110,000.

Abin damuwa shine, mata masu ciki kashi 20 ne ke karbar maganin rigakafin kare wannan cutar, wanda ke hana yaduwar cutar daga iyaye zuwa jariri. Daga rahoton, har yanzu Nigeriya tana kusan kasan kashi daya bisan uku na dukan sabbin kamuwa da cutar HIV a cikin yara a kasashe 21 na saharar Africa – kasa mai yawan jama’a cikin dukan kasashe. Rutohon ya nuna cewa Nigeriya na fuskantar kalubale.

Wadansu binciken sun nuna cewa yawan matan da suke kamuwa da HIV tsakanin 2009 da 2012 basu sake ba a kasashe da yawa. Kasar Ghana (kashi 44) da Africa ta kudu (Kashi 28) suke da raguwa sosai a kan mata masu kamuwa da cutar HIV.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG