Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Banbanci Tsakanin 'Yan Bindiga Da ‘Yan Ta'adda - Sanata Bulkachuwa


Fulani masu garkuwa da mutane
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:17 0:00

Fulani masu garkuwa da mutane.

Sanata Adamu Bulkachuwa mai wakiltar mazabar jihar Bauchi ta Arewa ya bayyana cewa ba bu wani banbanci tsakanin 'yan fashin daji da' yan ta’adda domin duk suna aiki ne iri daya.

Sanata Bulkachuwa ya bayyana hakan ne a cikin wani shirin siyasa na gidan talabijin na Channels, inda ya ce akwai yiyuwar an yi hikima ne da ba su suna ‘yan bindiga da ake kiran su saboda yadda ake daukar ta'addanci a kasashen duniya a matsayin mafi munin laifin da kowane gungun mutane ke iya aikatawa.

A cewarsa, yan bindiga ma ‘yan ta’adda ne a zahiri don babu sunan da ya kamata a kira wanda ke tada zaune tsaye idan ba dan ta’adda ba.

A kiraye-kirayen baya-bayan nan kan ayyana ‘yan bindiga da masu daukar nauyinsu a matsayin ‘yan ta’adda, sanatan Bulkachuwa na daya daga cikin masu ruwa da tsaki a Najeriya da suka shiga fafutuka ta neman a ayyanasu a matsayin yan ta’adda.

Sanata Adamu Bulkachuwa mai wakiltar mazabar Bauchi ta arewa a tarayyar Najeriya
Sanata Adamu Bulkachuwa mai wakiltar mazabar Bauchi ta arewa a tarayyar Najeriya

Ko a ranar Lahadin da ta gabata ma, sai da babban lauyan nan mai mukamin SAN a Najeriya, Femi Falana ya yi kira ga kafafen yada labarai da ‘yan Najeriya da su daina kiran masu aikata laifuka a matsayin‘ yan fashi ko ‘yan bindiga, yana mai jaddada cewa su ‘yan ta’adda ne.

A cewar Falana, gwamnati ta hanzarta ayyana wadanda suka sace daliban makarantar sakandaren Chibok a jihar Borno da yan awaren IPOB masu rajin kafa kasar Biyafara a matsayin ‘yan ta’adda amma a bisa dalilan da ita kadai ta sani, ta ci gaba da kiran masu tada zaune tsaye, sace mutane don neman kudin fansa da kashe-kashe a yankin Arewa maso yamma a matsayin yan bindiga.

Kalaman na sanata Bulkachuwa da Femi Falana na zuwa ne kwanaki kadan bayan da majalisun dokokin kasar suka yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana ‘yan bindiga da masu daukar nauyinsu a matsayin yan ta’adda.

A cewar dan majalisar da ke wakiltar Bauchi ta Arewa, ya kamata gwamnati ta ayyana 'yan fashi da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa a matsayin ‘yan ta’adda, kuma ya yi imanin cewa hakan zai taimaka wajen yakar masu aikata muggan laifuka a cikin kasar.

XS
SM
MD
LG