Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Ma Bin Ka’idojin Amfani Da Kafofin Sada Zumunta – Masana


Wani taro da aka gudanar da nufin fadada amfanin shafin Facebook
Wani taro da aka gudanar da nufin fadada amfanin shafin Facebook

Wata sabuwar matsala da ke addabar wasu kasashe musamman ma masu taso wa, ita ce yadda ake amfani da kafofin sada zumunta na social media,ba tare da ka’ida ba, lamarin da ke kara ruruta wutar rikice-rikicen da ke faruwa.

Shafukan sada zumunta na social media na taka muhimmiyar rawa wajen samun labarai ko aika wa da sako a tsakanin al’umma.

Kafofi irinsu Facebook, Twitter, Badoo, Instagram, Google Plus,Whatsapp kan samar da labarai tare da sada zumunta cikin sauki.

Sai dai yayin da a kasashen da aka ci gaba akan yi amfani da wadannan kafofi ta hanyoyin da suka dace, a kasashe masu tasowa da alamun ba haka labarin yake ba.

Arch. Sa’adatu Aminu Raji, malama a babbar kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Adamawa, wato Adamawa state Polytechnic, ta ce, wasu har yanzu ba su iya amfani da wadannan kafofi ta yadda ya kamata ba.

A cewarta maimakon samun ilimi, labari ko fasaha, wasu sun koma yada karya da ta da husuma.

Shi ko Malam Muhammad Lawal Danladi, ya ce abun mamaki wasu sun yi amfani da hotunansu lokacin da aka samu tashin bam, wanda ya rutsa da su a massalacin kwalejin, wajen nuna hotunansu a matsayin daya daga cikin hotunan rikicin yankin Mambilla a jihar Taraba.

A cewar Malam Dandali, wannan abun ya ba shi mamaki.

Saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz domin karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:08 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG