Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Majalisar Harkokin Da’awa Ya Nemi Hadin Kan Addinai


تھائی لینڈ کے سمندر سے پرانا جال نکالنے کے لیے کیے گئے آپریشن میں 40 غوطہ خوروں نے حصہ لیا۔

Majalisar kula da harkokin Da'awa ta Kasa ta kamala wani taron koli na wuni biyu da ya hada kan shugabannin majalisar da sarakunan gargajiya da na addinai daga dukan shiyoyin Najeriya, inda aka yi nazarin matsalolin dake shafar zamantakewa musamman da ya shafi banbancin addini,

A cikin hirarsu da Sashen Hausa shugaban kungiyar hadakar matasa Musulmi Mamman Lawal Mai Doki ya bayyana cewa, an shirya taron ne ganin yadda ake kara fuskantar kalubalar zamantakewa, inda ake fuskantar rashin jituwa da tashe tashen hankali tsakanin Musulmi da Kirista. Yace wannan taron zai bada damar fahimtar juna kasancewa ya hada kan mutane daga kabilu da addinai dabam dabam, Yace taron ya nemi bin tsari da magabata suka kafa kasar a matsayin kasa daya dunkulalliya.

Mahalarta taron da dama da Sashen Hausa ya yi hira da su, sunce wannan taron yazo daidai lokaci da ya dace musamman ganin yadda ake kara zaman doya da manja tsakanin Musulmi da Kirista, yayinda ake fama da rikicin Fulani da Makiyaya da kuma rikicin Boko Haram, da na ‘yan bindigar Niger Delta duk da yake wancan ya dan lafa, sai dai a matsayin kasa baki daya ana fuskantar kalubalar tsaro, da rikice rikicen da ake dangantawa da harkar siyasar kasar.

Shugaban kula da harkokin Da’awa na shiryar Kudu maso Kudu da kuma kudu maso gabashin kasar Uztaz Mohammad yace a daidai lokacin da ake neman mafita tsakanin Kiristoci da Musulmin najeriya akwai bukatar taro irin haka da zai taimaka wajen dinke baraka

Taron da aka saba gudanarwa duk shekara, ya sami halartar mai martaba Sarkin Musulmi Mahammad Sa’ad Abubakar , da shugabannin addinin Kirista, da kuma wadansu shugabannin al’umma daga arewacin kasar, inda aka gabatar da jawabai da kasidu

Wadanda suka gabatar da kasidun da suka hada da Limaman Kirista da Musulmi da kuma sarakunan gargajiya sun maida hankali a jawabansu kan bukatar zaman lafiya inda aka jadada bukatar Kirista da Musulmi su rungumi juna.

Ga cikakken rahoton Lamido Abubakar.

taron shugabannin addini da sarakunan gargajiya-3:45"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG