Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Ma Goyon Bayan Raba Kasa - Tinubu, Shugabannin APC Na Kudu Maso Yamma


Taron Shugabannin APC Na Yankin Kudu Maso Yamma

Tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigo a jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya Bola Ahmed Tinubu, da dukan shugabannin jam’iyyar a yankin kudu maso yamma, sun bayyana rashin goyon bayansu akan kiraye-kirayen da ake yi na raba kasar Najeriya.

A wani taro da suka gudanar a birnin Ikko da yammacin Lahadi, wanda ya sami halartar gwamnonin kudu maso yamma, da kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, da Cif Bisi Akande da shi kan sa jigon na APC Bola Tinubu, duk sun yi muwafaka akan dagewarsu na tabbatar da ci gaban hadin kan kasa.

Haka kuma sun jaddada goyon bayansu ga ci gaba da kasancewar Najeriya kasa daya, suka kuma yi kira ga samun hadin kai tsakanin kabilu da mabiya addinai daban-daban, tare da bayyana cewa ballewa domin kafa sabuwar kasa ba zai haifar da da mai ido ba.

Shugabannin sun yi tir, tare da nuna adawarsu akan masu fafutukar ballewa da furta kalaman nuna kyama da wariya, inda suka yi kira ga masu wadannan halayyar da su daina, su kuma rungumi dabi’ar zama lafiya, hadin kai da kuma dorewar Najeriya a zaman kasa daya.

To sai dai kuma taron ya goyi bayan matakin haramta kiwon dabbobi a sarari, kamar yadda gwamnonin yankin kudancin Najeriya suka yi matsaya a wani taro da suka gudanar a birnin Asaba ta jihar Delta a ranar 11 ga watan nan na Mayu.

Sun ce sun yi hakan ne kuwa domin suna ganin matakin zai rage tashin hankali tsakanin manoma da makiyaya, haka kuma zai taimaka wajen samun dawwamammen zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki, musamman tsakanin al’ummomin manoma da na makiyaya.

Akan haka suka yi kira ga gwamnati tarayya da gwamnatocin jihohi, da su hada kai wajen samar da hanyoyin kiwon dabbobi na zamani, ta yadda manoma da makiyaya za su yi al’amuransu ciki tsanaki da inganci.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar kalubalen tsaro a dukkan sassan kasar, a yayin da kuma ake sabunta kiraye-kirayen raba Najeriya, ciki har da masu hankoron ballewa domi kafa kasar Yarbawa a kudu maso yammacin Najeriya.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG