Accessibility links

Ba Mu Hana Jiragen Qatar Airlines Sauka A Kano Ba


Wani jirgin saman kamfanin safarar jiragen Qatar "Qatar Airlines" a wani filin jirgin kasar Burma

Wani mukarrabin ministar kula da zirga-zirgar jiragen saman Najeriya, Stella Oduah, yace babu gaskiya cikin labarin cewa sun hana jirgi zuwa Kano

Wani mai magana a madadin ministar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya, Madam Stella Oduah, ya musanta rahotannin dake cewa ma'aikatar ta hana ma kamfanin safarar jiragen saman Qatar Airlines iznin sauka a Kano.

Mr. Joe Obi, daya daga cikin mashawartan ministar, ya ce a maimakon haka ma, ministar ce take bin sawun wasu kamfanonin safarar jiragen sama domin su rika sauka da tashi a filin jirgin saman Malam Aminu Kano.

Idan ba a mance ba, wasu kafofin labarai a Najeriya sun bayyana cewa ma'aikatar kula da zirga-zirgar jiragen saman Najeriya ta ki yarda ta ba kamfanin Qatar Airlines iznin sauka a Kano da Abuja, a maimakon haka sai aka nemi kamfanin ya rika sauka a Enugu da Port Harcourt, watau yankin da ita ministar ta fito.

Kafin nan ma, an sha yayata rahotannin cewa Mrs. Oduah, ta hana kamfanonin jiragen saman Emirates, Turkish da Etihad iznin sauka a Kano a farkon wannan shekara, kuma ta nemi karkata su zuwa Enugu da Port Harcourt.

Da yake kare ministar, Mr. Obi yace ministar ta yi ta bin sawun kamfanin jiragen saman Emirates da ya rika sauka a Kano, amma har yanzu kamfanin bai yarda ba. A cewarsa, duk kamfanin jiragen saman dake son sauka a Kano, zai samu iznin ma'aikatar cikin gaggawa.

Amma wasu majiyoyi da yawa masu alaka da harkar zirga-zirgar jiragren sama a Najeriya sun ce a zahiri, kamfanin na Qatar Airlines yana da iznin sauka sau 7 cikin mako guda a Kano karkashin yarjejeniyar zirga-zirgar jiragen sama tsakanin Najeriya da Qatar ta 2008, amma da yaje ya nemi a kyale shi ya fara aiki da wannan iznin, sai ministar ta ki yarda.

Ladan Ibrahim Ayawa ya aiko mana da karin bayani.

XS
SM
MD
LG