Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Mu Kwatanta Igboho Da Annabi Muhammadu Ba - Afenifere


Kungiyar Yarbawa ta Afenifere

“Kafafen yada labarai da dama sun buga labarin, amma me ya sa babu wanda ya rubuta wannan kwatancen sai Sahara Reporters? Wannan kage ne kawai, domin sam ba shi ne gangar jikin kan labarin da suka wallafa ba” in ji Afenifere.

Kungiyar Yarbawa zalla ta Afenifere ta nisanta kan ta da labarin da jaridar yanar gizo ta SAHARA REPORTERS ta wallafa, da ke kwatanta arcewar Sunday Igboho mai fafutukar kafa kasar Yarbawa da hijirar Annabi Muhammad S.A.W.

Sahara Reporters ta wallafa labarin wata sanarwa da kungiyar ta Afenifere ta fitar tana yabawa basarake Olubadan na Ibadan Salisu Adetunji da kuma Ooni na Ife, Adeyeye Ogunwusi, saboda goyon bayansu akan Sunday Igboho.

A labarin da ta wallafa a shafinta na yanar gizo, jaridar ta Sahara Reporters ta ruwaito cewa kungiyar ta Afenifere ta kwatanta “gudun da Igboho yayi daomin tserewa jami’an tsaro tamkar hijirar da Annabi Muhhamdu ya yi ne daga Makka zuwa Madina domin kaucewa muzgunawa.”

Labarin da Sahara reporters ta wallafa a Facebook
Labarin da Sahara reporters ta wallafa a Facebook

Wannan lamari ya janyo cece-kuce da kuma martani mai zafi musamman daga yankuna daban-daban na musulmai a Najeriya.

To sai dai kuma kungiyar ta Afenifere ta sake fitar da wata sanarwa, tana nisanta kan ta da wannan labari, tare kuma da yin Allah wadai da jaridar ta Sahara Reporters.

A cikin sanarwar da sakataren watsa labarai na kungiyar, Jare Ajayi ya fitar, Afenifere ta ce “muna son tabbatarwa karara cewa Afenifere ba ta yi wannan kwatancin ba ta ko wane nau’i.”

Ta kara da cewa Afenifere kungiya ce da ke da mambobi daga addinai daban-daban, kuma akasarin manyan shugabanninta musulmai ne, don haka ba yadda za’a yi ta furta wani kalami da kan iya kasancewa suka ko batanci akan ko wane addini.

To sai dai kungiyar ta bayyana gaskiyar labarin na sanarwar ta ta farko da ta fitar a ranar 25 ga watan Yuli, inda take yabawa sarakunan biyu akan aikewa da wakilansu domin su shaidi zaman shari’ar Sunday Igboho a birnin Cotonou na kasar Jamhuriyar Benin.

“Mun bayyana cewa abin damuwa ne yadda gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta maida hankali wajen farauta da hantarar wadanda ke neman sauki daga mawuyacin halin da Najeriya take ciki, a maimakon fuskantar hanyoyin magance matsalolin sace-sacen mutane da ayukan ta’addanci da kuma tashe-tashen hankulan da ke da nasaba da kabilanci.”

Ta ci gaba da cewa “dangane da gudun da Sunday Igboho ya yi kuwa, mun ce wannan ba bakon al’amari ne kuma ba laifi ba ne domin a tarihin magabata ma wasunsu sun yi kokarin neman mafaka a wani wurin.”

Sunday Igboho
Sunday Igboho

“Mun ba da misalai biyu, na farko shi ne yadda Annabi Musa ya gujewa ukubar Fir’auna a Masar, na biyu kuma Annabi Muhammad ma ya bar garinsa na haihuwa wato Makka ya koma Madina domin gujewa tsangwama, don haka ba wani laifi ba ne don Sunday Igboho ya gudu domin kariyar rayuwarsa.”

Kungiyar ta jaddada cewa ta ba da misalan ne kawai don jadda tarihi, amma ko kadan ba tana kwatanta gudun na Igboho da hijirar wadannan annabawa ba.

“Kafafen yada labarai da dama sun buga labarin, amma me ya sa babu wanda ya rubuta wannan kwatancen sai Sahara Reporters? Wannan kage ne kawai, domin sam ba shi ne gangar jikin kan labarin da suka wallafa ba” in ji Afenifere.

Sanarwar ta ci gaba da cewa “muna yin Allah wadai da wannan labarin da jaridar ta wallafa duk da yake ta goge shi a shafinta tare da neman afuwa. Idan da labarin yana da kamshin gaskiya, me zai sa har jaridar ta goge shi, ta kuma ba da hakuri?”

Sahara Reporters ta nemi afuwa
Sahara Reporters ta nemi afuwa

Afenifere ta jaddada matsayar ta na girmama dukkan Annabawa musamman Annabi Muhammad, kasancewar ta mai membobi mabiya adinai daban-daban.

Har kawo yanzu dai ana ci gaba da mai da martani kan wannan labarin na jaridar ta Sahara reporters ta yanar gizo, duk kuwa da cewa tuni da ta cire labarin daga shafinta, ta kuma nemi afuwa kan wallafa shi.

XS
SM
MD
LG