Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Mu Yi Cikakken Bayani Kan Raunin Jirgin 737 MAX Ba - Boeing


Tun bayan hadurran da suka faru guda biyu, daya ga jirgin kasar Indonesia a bara da kuma dayan da ya faru cikin watan Maris a kasar Habasha, masu bincike sun yi imani wata na'urar gargadi ta taka rawa.

Shugaban kamfanin Boeing, Dennis Muilenburg, ya amince cewa kamfanin ya tafka “kuskure” na kin yin cikakken bayyani ga kamfanonin jiragen sama da matuka jirge, da kuma jami’an da ke saka ido akan wata fitila da ke nuna alama ta gargadi a jiragen 737 MAX 8 da aka dakatar da amfani da su.

Masu bincike sun yi imanin cewa fitilar gargadin wacce ke sashin matuka jirgi, tana hade da wata na’ura da ta taka rawa a munanan hadurran da suka faru na jiragen 737 MAX guda biyu – inda daya ya faru a kasar Indonesia a bara da kuma dayan da ya faru a kasar Habasha a watan Maris – wanda ya halaka mutum 356.

Muilenburg ya fadawa manema labarai a wajan wani bikin nuna jiragen sama a Paris jiya Lahadi cewa, kamfanin Boeing ba ya tattaunawa akai-akai tare da wadanda suka sayi jiragen, inda ya ce, wannan abu ne da ba za a lamunta ba.

Ya kuma kara da cewa kamfanin Boieng ya shiga wani hali na abin kunya.

Sannan ya yi alkawarin cewa kamfani zai zama mai bayyana gaskiya a nan gaba, kuma zai himmatu wajen ganin ya sake janyo hankulan kwastomominsa, yayin da yake kokarin inganta jirgin na MAX 737 domin a ci gaba da amfani da shi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG