Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Na So Na Sake Ji An Ce “Wasu ‘Yan bindiga Da Ba A San Ko Su Waye Ba” – Lalong

Gwamnan jihar Filato Simon Lalong (Facebook/Gwamnatin Filato)
Gwamnan jihar Filato Simon Lalong (Facebook/Gwamnatin Filato)

A ‘yan kwanakin nan an yi ta kai hare-hare a kewayen jihar, wadanda suka yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Gwamnan jihar Filato da ke tsakiyar arewacin Najeriya Simon Lalong, ya yi kira ga jami’an tsaro da suka kara zage damtse wajen dakile hare-haren ‘yan bindiga a sassan jihar, yana mai nuna damuwa kan yadda ake kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Lalong ya yi kiran ne yayin da Babba Sifeton ‘yan sandan Najeriya, Alkali Baba ya kai ziyara jihar don kaddamar da wasu kayayyakin aiki ga jami’an tsaro da hukumomin Filato suka tanada.

Gwamna Simon Lalong da Sifeton 'yan sandan Najeriya Alkali Baba(Facebook/Gwamnatin Filato)
Gwamna Simon Lalong da Sifeton 'yan sandan Najeriya Alkali Baba(Facebook/Gwamnatin Filato)

Duk da cewa muna alfahari da irin ayyukan da hukumomin tsaro ke yi wajen dakile hare-hare da sauran muggan ayyuka, Gwamna Lalong ya nuna damuwarsa kan yadda aka gaza kaucewa wasu hare-hare da ake kai wa a wasu yankuna.” Wata sanarwa da Darektan yada labaran gwamnati Dr. Makut Simon Macham ta ce.

A ‘yan kwanakin nan an yi ta kai hare-hare a kewayen jihar, wadanda suka yi sanadin mutuwar mutane da dama.

A lokuta da dama akan ce wasu 'yan bindiga da ba san ko su waye ba ne suke kai hare-hare, abin da gwamnan ya ce ba ya so ya sake ji.

Motocin jami'an tsaro da Gwamnatin Filato ta samar (Facebook/Gwamnatin Filato)
Motocin jami'an tsaro da Gwamnatin Filato ta samar (Facebook/Gwamnatin Filato)

Lalong ya kuma fadawa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaron cewa, “ba na so na sake jin ana cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba a jihar Filato.”

Gwamnatin ta jihar Filato ta kaddamar da sabbin motocin ‘yan sanda guda 50 da babura 200 a bikin da aka yi a ranar Litinin a fadar gwamnatin jihar da ke yankin Ray Field.

Wasu daga cikin baburan da jihar Filato ta ba rundunar 'yan sandan jihar (Facebook/Gwamnatin Filato)
Wasu daga cikin baburan da jihar Filato ta ba rundunar 'yan sandan jihar (Facebook/Gwamnatin Filato)

Lalong ya kara da cewa, gwamnatinsa ta yi abin a zo gani wajen rage aukuwar tashe-tashen hankula a jihar, abin da ya ce ya ba al’umar jihar kwarin gwiwa da kuma janyo hankulan masu saka hannayen jari.

Yayin jawabinsa, babban sifeton ‘yan sanda na kasa Alkali Baba, ya yaba da irin matakan da gwamnatin Filato ta dauka na karfafa fannin tsaronta.

Ya kuma ba da tabbacin cewa ana shirin daukan karin jami’an tsaro a kasar da kuma samar da horo na musamman don karfafa tsaron Najeriya.

XS
SM
MD
LG