Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Tabbacin Ci Gaba Da Zamana A Inter - Conte


Antonio Conte
Antonio Conte

Antonio Conte ya ce babu tabbas akan ci gaba da zamansa a kungiyar Inter Milan

Mai horar da ‘yan wasan kungiyar Inter Milan ta kasar Italiya Antonio Conte ya bayyana tababa akan ci gaba da aikin horar da ‘yan wasan kungiyar a kakar wasanni mai zuwa, biyo bayan kashin da kungiyar ta sha a wasan karshe ta gasar Europa League a jiya Juma’a.

Kungiyar Sevilla ce ta yi nasarar doke Inter din da ci 3-2, a yayin da dan wasan Inter din Rumelu Lukaku ya sha kansu, ya jefa kwallon da ta baiwa Sevilla din nasara, ta kuma lashe kofin na gasar ta Europa ta bana.

Antonio Conte ya yi kokarin ganin kungiyar ta sami lashe ko da akalla gasa daya a wannan kakar wasannin, to amma hakan bai samu ba.

Kungiyar ta soma fafata gasar Serie A ta kasar ta Italiya da karfin gaske, to amma kuma daga baya al’amuranta suka tabarbare, har Juventus ta lashe gasar ta bana.

Daga bisani tsohon kocin na Chelsea da yaran nasa sun mayar da hankali akan gasar Europa League tare da fatar daga kofin gasar, amma shi ma hakan bai samu ba.

Antonio Conte
Antonio Conte

Conte ya fadawa mujallar wasanni ta UK Sun cewa yanzu haka dai yana nan yana Nazari, tare da duba tudun dafawa a sabuwar kakar wasanni mai zuwa.

Facebook Forum

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG