Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Za A Kara Kudin Fetur A Watan Mayu Ba - NNPC


Shugaban NNPC, Malam Mele Kyari
Shugaban NNPC, Malam Mele Kyari

Najeriya na kashe biliyoyin daloli wajen samar da tallafin mai, wani abu da Bankin Duniya ke so kasar ta kawar idan har tana son samun bashi daga bankin.

Kamfanin mai na NNPC a Najeriya, ya ba da tabbacin cewa ba zai kara kudin litar man fetur a watan Mayu ba.

Shugaban kamfanin Malam Mele Kyari ne ya bayyana hakan a shafin sada zumuntar kamfanin na Twitter.

“Ba za a kara kudin litar mai ba a watan Mayun shekarar 2021.” Sakon na NNPC ya ce.

Wannan sanarwar ta kore duk wata jita-jita da ake yadawa, cewa za a kara kudin litar man wacce take a naira 166 a yanzu.

An ga dogayen layin shan mai a wasu manyan biranen Najeriya ciki har da Abuja, inda mutane suka yi ta rige-rigen sayen man gudun kada a shammace su da sabon farashi.

A kusan tsakiyar watan Maris, hukumar da ke kayyade farashin man fetur ta PPPRA a kasar, ta wallafa wasu bayanai da ke nuni da yadda za a kara farashin litar man fetur da zai kai kusan 206.

Hakan ya janyo suka daga jama’ar kasar ya kuma sa wasu gidajen mai suka tsawwala farashinsu.

Hedikwatar NNPC a Abuja, Najeriya
Hedikwatar NNPC a Abuja, Najeriya

Amma bayan da kamfanin na NNPC ya musanta bayanan karin farashin, hukumar ta PPPRA ta janye bayanan da ta wallafa.

Najeriya dai na kashe biliyoyin daloli wajen samar da tallafin mai, wanda na daya daga cikin sharuddan da bankin duniya ke so kasar ta kawar kafin ta sami bashi daga bankin.

Sai dai cire tallafin, na nufin jama’ar kasar za su rika sayen man da tsada.

XS
SM
MD
LG