Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Za A Yi Taron G-7 A Doral Ba - Inji Shugaba Trump


Trump National Doral

A wasu jerin sakwannin Twitter da daren jiya Asabar, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya soke shirin karbar bakuncin taron manyan kasashe na G-7, a wani wurin shakatawa na wasan Golf da ke Miami, jahar Florida.

A farkon wannan satin Shugaba Trump ya tabbatar da shirin gudanar da taron a wurin, wanda ake kira Trump National Doral.

Ya dora laifin hakan ga kafafen yada labarai, da kuma ‘yan jam’iyar Demokarat, wadanda ya ce sun nuna dawa da shirin yin taron a Doral.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG