Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Zan Cika Wa'adina Ba Idan Aka Zabe Ni a Karo Na Biyar - Bouteflika


Yadda mutane suka fita kan tituna suna zanga zangar neman shugaba Bouteflika ya sauka a mulki

Shugaban kwamitin yakin neman zaben Bouteflika, Abdelghani Zaalane ya ce shugaban zai sake kiran wani sabon zabe a cikin shekara daya idan ya lashe zabe a karo na biyar.

Dadaddan shugaban kasar Algeria, Abdelaziz Bouteflika ya fada jiya Lahadi cewa idan aka sake zaben shi a watan Afrilu ba zai cika wa’adin mulkin ba.

Shugaban mai shekaru 82 ya bayyana hakan ne yayin da ake ci gaba da yin zanga zanga kan aniyarsa ta sake neman wani wa’adin mulki a karo na biyar.

Shugaban kwamitin yakin neman zaben Bouteflika, Abdelghani Zaalane ya ce shugaban zai sake kiran wani sabon zabe a cikin shekara daya idan ya lashe zabe a karo na biyar.

Zaalane ya sanara da hakan ne a wani jawabi da ya yi a gidan talabijin bayan da ya mika takardun shugaban dan shekaru 82 da haihuwa da suka tabbatar da aniyarsa ta shiga zaben da za’a yi a watan Afrilu.

Bouteflika wanda ya kai ziyara kasar switzerland a ranar Lahadi domin duba lafiyarsa, ya karbi shugabancin kasar ta Algeria ne tun a shekarar 1999.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG