Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Zan Kara Durkusawa Kafin Wasa Ba - Zaha


Dan Wasan Crystal Palace Wilfried Zaha

Dan wasan gaba na kungiyar Crystal Palace Wilfried Zaha ya ce zai daina gurfanawa a gwiwarsa kamar yadda ake yi kafin buga kowace wasan gasar Premier, domin karfafa fafutukar “Rayuwar Bakar Fata na da Muhimmanci.”

Zaha mai shekaru 28 da haihuwa, ya fadawa kafar yada labarai ta BBC cewa wannan durkuson tamkar wani "kaskanci" ne, a inda ya kamata a ce suna tsaye kaimun domin kare kima da martabar bakaken fata.

Hukumar shirya gasar Premier ta Ingila, na daga cikin hukumomin da suka tsara ‘yan wasa su rika gurfanawa a kan gwiwar kafar su, domin nuna goyon baya ga fafutukar nan ta ‘Black Lives Matter’ wadda aka soma tun bayan mutuwar Ba’amurke George Floyd, sakamakon danne masa wuya da wani dan sanda farar fata yayi.

Dan Wasan Crystal Palace Wilfried Zaha
Dan Wasan Crystal Palace Wilfried Zaha

Zaha ya ce wannan “tamkar muna ware kan mu ne bisa wani tsari da bai da amfani.”

A makon jiya ma Zaha ya saka ayar tambaya akan makasudin gurfanawa da ‘yan wasa suke yi a gwiwar kafar su kafin soma wasa.

Ya ce “ina dalilin cewa har sai mun laka tambarin Black Lives Matter a rigunanmu, domin mu nuna cewa mu (bakaken fata) muna da muhimmanci? Wannan kaskanci ne da faduwar girma.”

Dan Wasan Crystal Palace Wilfried Zaha
Dan Wasan Crystal Palace Wilfried Zaha

Da yake jawabi a wani taron bunkasa kasuwanci a sha’anin kwallon kafa, Zaha ya ce iyayensa sun tarbiyyantar da shi akan alfahari da kasancewarsa bakar fata, don haka zai tsayu ne kaimun akan haka, ba wai durkusawa ba.

Ya kara da cewa ya gaji da yadda ake amfani da shi a matsayin wata kafa ta yaki da wariyar launin fata, wanda ya kamata a dauki kwararan matakai na kawar da shi a duniya.

A wannan makon kuma kungiyar Brentford ta ce ‘yan wasan ta za su daina yin gurfanin kafin wasa, saboda suna ganin cewa yin hakan a yanzu bai da wani tasiri a fafutukar yaki da nuna wariya.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG