Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Bankin Amurka Ba Zai Kara Kudin Ruwa Ba Domin Habakar Tattalin Arziki


Shugabar Babban Bankin Amurka, Janet Yellen
Shugabar Babban Bankin Amurka, Janet Yellen

Jamian bankin suka ce, kasuwanci na kara bunkasa, yayin da kashe kudi sai karuwa yake yi, amma kuma kasuwanci yana nan ba yabo ba fallasa, haka kuma hauhawan farashin kayayyaki na nan kasa da abinda ake tsammani.

A cikin wani bayani da bankin ya fitar yace bukatar kara kudin ruwa na karakarfi amma kuma shugabannin suna son su samu kwakkwarar hujjar yin hakan.

Babban bankin dai ya rage kudin ruwa lokacin da aka shiga matsin tattalin arziki da ya shafi duniya kuma sunyi hakan ne da niyyar ganin an samu bunkasar tattalin arziki a cikin watan Disamba lokacin babban bankin ya dan kara kudin ruwa kadan wanda yake har yanzu yana kasa-kasa sosai.

XS
SM
MD
LG