Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Bankin Najeriya Ta Raba Gari Da 'Yan Canji


Nigeria Currency
Nigeria Currency

Yanzu dai abun jira shine ko matakin da kungiyar ‘yan canjin ke shirin dauka zai haifar da dan mai ido

Kasa da sao’i, 48, bayan da babban bankin tarayyar Najeriya, tace ta raba gari tsakaninta da ‘yan canji a Najeriya, yanzu haka dai farashin dalar Amurka ya kai Naira 300, akan kowace dala 1.

Alamarin da ya nuna Karin kusan Naira 50, akan yadda ake sayar dashi a can ba tuni dai kungiyar ‘yan canji ta Najeriya, ta bayyana rashin jindadinta dangane da wannan mataki da babban bankin tarayyar Najeriya, ta dauka .

Kungiyar tace matakin yayi tsauri matuka, Alhaji Aminu Gwadabe shugaban kungiyar ‘yan canji a tarayyar Najeriya, yace a halin gaskiya wanna mataki ya kawo raunana farashin Naira a cikin kasuwa, a cikin kwana 2,darajan Naira ya karye da sama da Naira 30,yanzu haka a kasuwa mutane ‘yan kasuwa masu sayo kaya daga kasashen waje suna nemata a Naira 300,ma basu samu ba.

Sai dai kuma kungiyar ‘yan canjin ta bayyana cewa abunda yafi damunta shine bayan mari kuma harda tsinkamata jaka ganin yadda aka dora laifin tabarbarewar hada hadan kudaden kasar akan ‘yayan kungiyar.

Yanzu dai abun jira a gani shine ko matakin da kungiyar ‘yan canjin ke shirin dauka tare da tattaunawa da babban bankin Najeriya, da kuma ‘yan majalisun kasar zai haifar da dan mai ido, inko bahaka ba Nairar zata ci gaba da tabarbarewa , masamman idan akayi la’akari da karyewar darajar albarkatun mai da Najeriya, ta dogara dashi wajen samun kudaden shiga.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

XS
SM
MD
LG