Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Bankin Najeriya Ya Dauki Matakin Kara Yawaitar Dalar Amurka a Kasar


Garabasa ga masu shigar da kudi Najeriya, daga kasashen ketare.

Babban Bankin Najeriya (CBN), ya gabatar da wani shiri mai taken “Naira 4 Dollar” ga masu aikawa da dalar Amurka zuwa Najeriya.

A cewar babban bankin, manufar ita ce ta ci gaba da samun karin kudaden da ake shigo da su daga kasashen waje zuwa cikin kasar, wanda ‘yan kasar mazauna kasashen wajen kan aiko ga ‘yan uwansu da abokan arziki da ke Najeriyar.

Ana kuma sa ran shirin zai kwadaitar da turo kudaden waje zuwa Najeriya ta hanyar aikawa da kudade a hukumance wanda hakan zai taimaka wajen samar da daidaito ga kasuwar canjin kudade a kasar kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wannan sabon tsari zai rika dorawa masu aika dala naira biyar akan kowacce dala daya.

Wata sanarwa da babban darekta a sashen kula da cinikayya da canja kudade, Saleh Jibrin ya fitar, ta ce tsarin zai fara aiki ne tsakanin ranar 8 ga watan nan na Maris zuwa 8 ga watan Mayu na wannan shekara a cewar jaridar yanar gizo ta SolaceBase.

Akan duk wata Dala guda daya da ta shigo Najeriya ta hanyar Kungiyar canjin kudi ta duniya, Bankin CBN ta bankunan kasuwanci daban-daban a kasar zasu baiwa mai karban kyautar N5.

A takaice, akan kowane dala 1 da ka karba, za ka samu karin N5. Misali, idan ka karbi $100, za ka samu kyautar N500 kari akan kudinka.

Wannan ba tare da la'akari da ko ka karbi kudin ta kudin Najeriya, ko kuma an baka ta kudin kasashen wajen da aka aiko maka da kudin ba.

Wannan tsarin shine a biya masu karba ko sun zabi karbar Dalar Amurka a matsayin tsabar kudi a duk banki ko kuma canza su zuwa asusunsu na gida.

Sai da babban bankin na CBN ya ce shi zai dauki ragamar ba da garabasar ta N5 ba bankunan kasuwanci daban-daban na kasar ba.

Abu mai ban sha'awa anan shi ne, kyautar N5 kyauta ce ga dukkan bangarorin biyu, wato, mai aikawa da mai karba za su ji dadin wannan garabasar ta N5.

A zahiri, mai karba daga kasashen waje zai karba a lokacin karbar, ba kawai dala da aka turo daga kasashen waje ba, har ma da karin N5 akan kowacce dala daya da aka karba kamar yadda jaridar ta Daily Trust ta ruwaito.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG