Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Bankin Najeriya Ya Karyata Batun Jabun Kudi


Takardun kudin Naira na Najeriya

Babban bankin Najeriya na CBN ya musanta zargin da tsohon Mataimakin gwamnan bankin, Dr. Obadiah Mai Lafiya  ya yi na cewa kashi 20 na kudaden dake yawo a kasar kudaden jabu ne.

Mailafia, ya yi wanan furucin ne a lokacin da yake bada bahasi a gaban kwamitin kula da harkar kudade na majalisar tarayyar Najeriya.

Ya ce ma'aikatan Babban Bankin Najeriya sun san da haka kuma har suna cuwa- cuwa idan an mayar da tsofafin kudi.

Sai dai jami’an babban bankin Najeriya mai kula da hulda da jama’a, Isaac Okarafo, ya ce kididdigar da bankin ya gudanar daga watan Janairu zuwa Disambar shekara ta 2016, ta nuna cewa akwai kudaden jabu da yawansu bai kai kaso daya bisa dari ba.

kamar yadda ya ce kashi dayan na nufin za a iya samun takardun jabun kudi 14 daga cikin kowacce Naira miliyan daya da babban bankin ya buga.

Sai dai ya ce kamar kowacce kasa a duniya ba za a rasa kudaden jabu a Najeriya ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG