Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Hafsan Sojin Kasa Na Najeriya Janar Ibrahim Attahiru Ya Rasu A Hatsarin Jirgin Sama


Marigayi Janar Ibrahim Attahiru (Twitter/HQNigeriaArmy)

Bayanai sun yi nuni da cewa mutum 8 ne a cikin jirgin, yayin da wasu ke cewa mutum 12 ne.

Rahotanni daga Najeriya na cewa babban hafsan sojin kasa na Najeriya Laftanar Janar Ibrahim Attahiru ra rasu a wani hadarin jirgin sama da ya auku a yankin jihar Kaduna.

Cikin wata sanarwa da ta wallafa, rundunar sojin saman Najeriya a ranar Juma’a ta tabbatar aukuwar hadarin amma kuma ba ta fadada bayananta ba.

Sai dai wata majiya kwakkwara daga rundunar sojin Najeriya, wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta tabbatar da cewa har da Janar Attahiru a hadarin jirgin.

Bayanai sun yi nuni da cewa mutum 8 ne a cikin jirgin, yayin da wasu ke cewa 12 ne.

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce tanba kan binciken musabbabin hadarin.

“Jirgin saman rundunar sojin Najeriya ya yi hadari da yammacin yau a kusa da filin tashin jirage na Kaduna. Amma babu masaniyar abin da ya haddasa wannan hadari.” Sanarwar wacce Air Commodore Edward Gabkwet ya sa hannu ta ce.”

A watan Janairun bana, Shugaba Muhammadu Buhari ya nada sabbin hafsoshin tsaron kasar, ciki har da Janar Attahiru.

Attahiru (tsakiya) yayin wani taron tsaron kasa da shugaba Buhari ya gayyace su a kwanan nan
Attahiru (tsakiya) yayin wani taron tsaron kasa da shugaba Buhari ya gayyace su a kwanan nan

Shi ne ya gaji Janar Tukur Yusuf Buratai.

Kusan wannan shi ne karo na uku, da jiragen sojojin Najeriya ke faduwa ko bata a cikin wannan shekara.

Karin bayani akan: Janar Ibrahim Attahiru, Boko Haram, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

A watan Fabrairun bana, wani jirgin sojin saman kasar ya fadi a yankin Abuja, babban birnin tarayyar kasar dauke da sojoji bakwai – dukkaninsu sun mutu.

Jirgin na hanyarsa ta zuwa kai dauki ne a lokacin ana neman daliban Jangebe da ‘yan bindiga suka sace a makarantarsu da ke jihar Neja wacce ba ta da nisa da Abuja.

Lokacin da Shugaba Buhari ya gana da shugabannin tsaron kasa. Janar Attahiru (dama)
Lokacin da Shugaba Buhari ya gana da shugabannin tsaron kasa. Janar Attahiru (dama)

Sannan a watan Afrilu, wani jirgin saman sojin Najeriya da ke kai wa dakarun kasa dauki a yakin da Najeriyar ke yi da mayakan Boko Haram, ya yi batan dabo.

Daga baya mayakan Boko Haram suka yi ikirarin su suka harbo jirgin, inda suka fitar da wani bidiyo da ya nuna mayakansu a inda jirgin ya fadi.

Amma rundunar sojin saman Najeriya ta musanta bayanan da ke cikin bidiyon.

XS
SM
MD
LG