Accessibility links

Bayan wasu kwanaki da ya kwashe yana fama da jinya a asibiti, Allah ya yiwa babban limamin garin Jos, Sheikh Balarabe Dawud rasuwa.

Rahotanni daga Jos babban birnin Jahar Filato a Najeriya na cewa babban limamin masallacin juma’a garin, Sheikh Balarabe Dawud ya rasu.

Majalisar kungiyar Jama’atul Nasril Islam, (JNI) reshen jahar ta tabbatar da rasuwar limamin wanda Allah ya yiwa rasuwa a yau Lahadi.

“Allah ya yiwa mai alfarma babban limamin garin Jos, Sheikh Balarabe Dawud rasuwa da zunnan.” Inji Jami’in yada labarai na JNI, Malam Sani Mudi.

A cewar Mudi, Sheikh Dawud ya yi fama da wata gajeruwar rashin lafiya na tsawon kwanaki takwas a asibiti da ke garin na Jos.

Limamin ya kwashe shekaru shida ne yana jagorantar salla a babban masallacin na Jos, in ji Mudi.

“A shekarar 2009 ya karbi limancin masallacin, bayan rasuwar marigayi Sheikh Sa’idu Hamajan, amma kafin nan ya dade yana na’ibin liman.”

A cewar Mudi, Sheikh Dawud ya bar darrusa da dama ga al’uma, kamar abubuwan da suka shafi nuna tsoron Allah da kishin kai da tsayawa a kan gaskiya, musamman inda ya karawa matasa kwarin gwiwa wajen yin kwaikwayo da wadannan darrusa.

Kafin zama limamin Jos, Sheikh Balarabe Dawud, ya yi aikin alkalanci tun a lokacin Lardi na tsohuwar Jahar Biniwe-Filato da Jahar Filato har zuwa lokacin da ya yi murabus.

A cewar Mudi, Sheikh Balarabe Dawud ya kasance mai biyayya wanda darasi ne da ya yi kokari ya dasa a zukatan mabiyansa.

“Musamman idan aka lura, ya yi biyayya a lokacin da shi ma ya ke na’ibin Liman ga marigayi Liman da hakuri, har kuma Allah ya kawo lokacin da shi ne ya ke shugabanci, wannan babban darasi ne da al’uma ya kamata su koya.”

Ga karin bayani a rahoton Zainab Babaji:

XS
SM
MD
LG