Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris, ya ba kwamishanonin ‘yan sandan kasar umurnin su janye duk wani dan sanda dake kare wani babban mutum ba kan ka’ida ba.
Babban sufeton yace dole ne su yi hakan kafin karshen wannan watan domin tabbatar da cikakken iko kan duk ‘yan sandan kasar.
Da yake bayyana ra’ayinsa akan wannan al’amari, Malam Sha’aibu Mungadi, wani mai sharhi, ya ce ba daidai bane a rinka ganin ‘yan sanda rike da jakunan matan sanatoci a kasuwa idan sun je sayen kaya ko yin cefane. Mungadi yace ko a gonakin manyan mutane ana kai ‘yan sanda suna tsaro yayinda ake barin talakawa zaune, ba tsaro. Ya ce ya taba ganin wani dan sanda da ya share shekaru goma yana aiki a gidan gwamna ba’a taba canza shi ba.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani
Facebook Forum