Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Alamar Ta'adanci A Harin Landan -'Yansanda


Wani dan asalin Somaliya ya kai hari da wuka a birnin Landan
Wani dan asalin Somaliya ya kai hari da wuka a birnin Landan

‘Yan sandan birnin London sun fada yau Alhamis cewa basu sami wata hujja da ke nuna alamun aikin ta’addanci a harin da aka kai a birnin ba, bayan da wani mutum dan kasar Somaliyya ya cakawa wata mata wuka, tare da raunata wasu mutane su 5 a tsakiyar birnin na London, amma sun ce ta yiwu harin na da nasaba da matsalar tabin hankali.

‘Yan sanda sun kame matashin dan shekaru 19 da haihuwa a filin Russel dake kusa da jami’ar London bayan da suka yi amfani da wata na’ura. Matashin da ba a kai ga bayyana sunansa ba yana hannun ‘yan sanda yanzu haka a wani asibiti dake birnin na London.

Shawarar baza ‘yan sanda dauke da makamai a kan titunan London na da muhimmanci sosai saboda galibin yan sandan kasar Burtaniyya basa daukar bindigogi—

Jami’an tsaro sun bayyana cewa matar da ta rasa ranta a harin, ‘yar shekaru 60 da haihuwa, ‘yar kasar Amurka ce. Jami’an kiwon lafiya na gaggawa sun yi inyarta a inda abin ya faru, amma jim kadan bayan aukuwar lamarin, ta rigamu gidan gaskiya. An sallami mutane 3 daga cikin wadanda da harin ya shafa a safiyar yau Alhamis daga asibiti, sai dai ba a san halin da sauran mutanen su 2 suke ciki ba.

XS
SM
MD
LG