Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Cigaba A Tattaunawar Neman Zaman Lafiya A Siriya


Taron neman zaman lafiya a Siriya

Jami'an da suka kasance wurin tattaunawar zaman lafiya tsakanin gwamnatin Siriya da kungiyoyin 'yan tawaye, sun ce ba a sami wani cigaba ba jiya Litini a rana ta farko ta tattaunawar, to amma za a cigaba da tattaunawar yau Talata.

Jami'an sun ce tattaunawar da ake a Astana babban birnin kasar Kazakhstan, wadda kasashen Rasha da Turkiyya ke daukar nauyinta, ba ta kai tsaye ba ce, bangarorin biyu na tattaunawa da juna ne ta wajen masu shiga tsakanin.

Tattaunawar da ake yi a birnin Astana ta fi mai da hankali ne kan yadda za a jaddada yarjajjeniyar tsagaita wuta ta kasa baki daya, wadda Rasha da Iran da Turkiyya suka taimaka aka cimma a watan Disamban bara, yarjajjeniyar da aka kiyaye a akasarin wurare cikin kasar ta Siriya.

Tattaunawar zaman lafiyar Siriya da aka yi a lokuta daban-daban a can baya, ciki har da ta baya-bayan nan da aka yi bara, ba su kawo wani cigaba na a zo a gani ba wajen kawo karshen tashin hankalin da aka fara tun watan Maris na shekarar 2011.

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG