Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Sojan Kasarmu Da Ya Kamu Da Covid-19 - China


Yayin da rundunonin soji a fadin duniya ke ganin dakarunsu na kamuwa da cutar Coronavirus, rundunar sojin kasar China ta PLA, da ke zaman rundunar soji mafi girma a duniya, ta yi ikirarin cewa babu cutar tsakanin sojinta.

“China ta tabbatar da cewa babu wanda ya kamu da cutar coronavirus a cikin sojojinta,” wannan shi ne taken babban labarin wata mujallar sojin kasar da aka fitar.

Sai dai babu wani sabon bayani da aka fitar kan cutar tun wancan lokacin.

Baya ga sojoji miliyan biyu da ke rundunar, haka kuma kasar tana da ‘yan sanda 800,000.

A lokacin da kasar ta yi fama da annobar cutar, an fitar da dubban sojoji da suka hada da ma’aikatan lafiya zuwa wuraren da cutar ta bulla domin su taimaka, ciki har da birnin Wuhan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG