Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Tabbacin China Ce Ta Yi Mana Kutse - Amurka


Kakakin Fadar White House Josh Earnest

Fadar White House a Amurka ta ce ba za ta yi hanzarin zartar da hukuncin cewa masu satar bayanan kasar China ne suka yi kutse a wata ma’aikatar kasar da ke tattara bayanan miliyoyin ma’aikatan da ke aiki a karkashin gwamnati ba.

Mai magana da yawun gwamnati, Josh Earnest, ya ce hukumar bincike ta FBI na ci gaba da bincike kan wannan kutse, yana mai cewa akwai sauran aiki a gaba kafin a tantance inda matsalar ta ke.

Da farko hukumomin tsaron kasar sun ce masu kutse daga China ne suka aikata wannan laifi wadanda ake tsammanin suna da alaka da gwamnatin kasar ta China.

Sai dai hukumar ta FBI ba ta bayyana yadda ta kaiga wannan matsaya na ganewa cewa China c eke da alhakin kutsen ba.

A yau Juma’a, Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar China, Hong Lei, ya yi fatali da wanna zargi lamarin da ya kwatanta a matsayin abin da bas hi da tushe, yana kai cewa ire-iren wadannan kutse ana gudanar da su ta ko’ina ba kuma da wuya a gane ko wake da alhakin yin kutsen.

Ofishin kula ma’aikatan kasar Amurka, y ace akalla ma’aikata miliyan hudu abin ya shafa wadanda suka hada da ma’aikata na yanzu da wadanda suka bar aiki.

Wannan kutse ana mai kallon mafi girma akan ma’aikatun gwamnati da aka gani a cikin ‘yan shekarun nan.

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG