Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Houthi Sun Sako Wani Dan Jarida Ba'amarike


John Kerry, sakataren harkokin wajen Amurka.

A kasar Yemen 'yan Houthi sun sako daya daga cikin mutane hudu da suke tsare dasu.

An saki wani dan jaridar Amurka da aka kama shi a Yemen, to amma har yanzu babu cikakken bayani game da kamun nasa, yayin da Amurka ta sha alwashin ganin an sako karin Amurkawan da ake tsare da su a kasar.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta bayyana dan jaridar da suna Casey Coombs, wanda aka yi amince yana cikin yan jaridar Amurka da har yanzu su ke cikin Yemen, tun bayan da yan tawayen Houthi su ka abka babban birnin kasar su ka hambare Shugaban kasar a farkon wannan shekarar, wanda ya sa sojojin waje kai dauki bisa jagorancin Saudiya.

An yada wani hoton Coombs jiya Litiniyana bisa gadon jinya, yayin da Jakadan Amurka a Oman Greta Holtz ke gaishe shi a Muscat.

Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Marie Harf ta ki ba da cikakken bayani kan wanda ya kama Coombs da kuma irin rashin lafiyar da ya ke fama da shi.

Labarin sakin na Coombs ya biyo bayan wani rahoton da jaridar Washington Post ta bayar cewa yan Houthi na tsare da wasu Amurkawa hudu a Sana'a babban birnin kasar ta Yemen.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG