Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Tabbas Akan Yawan Sojojin Da Amurka Zata Bari A Afganistan


US forces in Helmand Province of Afghanistan
US forces in Helmand Province of Afghanistan

Duk da rashin tabbas kan iya yawan sojojin da Amurka za ta bari a Afghanistan nan gaba, akasarin kwamandojin sojojin NATO sun ce ba su yi shirin janye dakarunsu daga kasar da yaki ya daidaita ba, a cewar Ciyaman din Kwamiti Din Sojojin NATO a jiya Laraba.

Petr Pavel ya gaya ma manema labarai a Hedikwatar NATO a Brussels cewa, "Akasarin 'yan NATO na ganin da bukatar su cigaba da barin adadin sojojinsu kamar na yanzu a Afghanistan." Ya ce wannan shawarar ta biyu bayan ittifakin da aka yi cewa, "Har yanzu ba a samu yanayin da ya cancanci ficewar NATO ba."

Shugaban Amurka Barack Obama na son rage sojojin Amurka a Afghanistan daga 9,800 zuwa 5,500 zuwa karshen wannan shekarar. Saboda yawan sojojin da Amurka ta girke a Afghanistan, NATO ta rasa matakan da za ta dauka nan gaba a Afghanistan, yayin da Amurka ke nazarin ko za ta rage sojojinta din ko a a.

"Mu na jiran shawara ta karshe ta abin da za a yi, saboda mu san abin da mu kuma za mu yi," a cewar wani jami'in NATO jiya Laraba.

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG