Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Wanda Coronavirus Ta Kashe A Najeriya Cikin Kwana Tara


Dr Abdu Samad, likita a Najrryia,(VOA/Gilbert Tamba)
Dr Abdu Samad, likita a Najrryia,(VOA/Gilbert Tamba)

Hukumomin kasar sun ce mutum miliyan 1.8 aka yi wa gwajin cutar a duk fadin Najeriyar.

Cikin kwana tara a jere, ba a samu wanda cutar coronavirus ta kashe ba a Najeriya, in ji hukumar da ke yaki da yaduwar cututtuka ta NCDC.

Hakan na nufin har yanzu adadin wadanda cutar ta kashe yana 2,061 kamar yadda yake cikin kwana tara.

Hukumar ta ce a ranar Laraba sabbin mutum 65 ne suka kamu da cutar a jihohin Lagos (41) Kaduna (6) Kano (3) Rivers (3) Plateau (3) Akwa Ibom(2) Imo (2) Oyo (2) Edo (1) Bauchi (1) Osun (1)

Yanzu mutum 164, 488 ne jimillar wadanda cutar ta harba a kasar wacce ya zuwa yanzu ta kama mutum miliyan 144 a duk fadin duniya yayin da mutum miliyan uku suka mutu.

A watan Fabrairun bara, Najeriya ta samu mutum na farko da ke dauke da cutar.

Hukumomin kasar sun ce mutum miliyan 1.8 aka yi wa gwajin cutar a duk fadin Najeriyar.

XS
SM
MD
LG