Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Badakalar Takardun Shaidar Karatu Na Bogi Tsakanin Ma’aikatan Hukumar ICPC


ICPC
ICPC

Akalla ma’aikatan hukumar ICPC 50 ne suka bayyana a gaban wani kwamitin hukumar kan tantance takardun shaidar karatu da bayanan hidima inda aka gano wasu kura-kurai a shekarun su da kuma takardun shaidarsu na kammala karatu.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da sauran manyan laifuffuka ta ICPC mai zaman kanta ta soma binciken wata babbar badakalar takardun shaidar kammala karatu na bogi da rage yawan shekaru, da ake zargin wasu ma'aikatanta.

Wata majiya ta bayyana cewa mambobin kwamitin na ICPC na neman hanyoyin rufa lamarin da ya shafi manyan ma’aikatan hukumar da dama da aka samu da hannu a aikata wannan laifin na amfani da takardun kamalla karatu na bogi da badakalar rage yawan shekaru wajen samun aiki kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A halin yanzu, akalla ma’aikatan hukumar ICPC 50 ne suka bayyana a gaban karamin kwamitin gudanarwar hukumar kan tantance takardun shaidar ma’aikata da bayanan hidima inda aka gano wasu kura-kurai a shekarunsu na haihuwa da kuma takardun shaidarsu na kammala karatu.

Rahotanni sun yi nuni da cewa aikin tantance takardun kammala karatun ma’aikata da bayanan aiki ya samo asali ne sakamakon wasu bukatu da suka taso bayan hukuncin da aka yiwa wani jami’in hukumar tsaron farin kaya ta kasa wato NSCDC kan yin amfani da jabun takardar shaidar karatu don tabbatar da samun matakin aiki na gaba.

Rahotanni sun yi nuni da cewa a watan Oktoba ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa da sauran manyan laifuffuka wato ICPC ta kama wani ma’aikacin hukumar tsaro ta NSCDC wato Idowu Olamide a bisa laifin yin amfani da takardar shaidar difloma ta jabu wajen samun karin girma a ofishinsa, lamarin da aka ce ya sanya jama’a suka bukaci a binciki ma’aikatan ICPC da irin wannan zargi.

A baya hukumar ICPC ta ce an sami wani Idowu Olamide da laifin mika takardun difloma na karya da gangan, wanda ya sabawa sashe na 25 sakin sashin na 1 na dokar cin hanci da rashawa da sauran laifuffuka na shekarar 2000 wanda aka hukunta a karkashin sashe na 25 sakin sashi na 1(b) na wannan dokar.

Wani ma’aikacin hukumar ICPC da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa fafutukar ganin cewa hukumar ICPC ta binciki takardun shaidar kamalla karatun ma’aikatanta ya kara ta’azzara ne biyo bayan batun wata tsohuwar ma’aikaciyar hukumar da ta bar ICPC zuwa hukumar NDIC amma daga baya aka kore ta daga aiki bayan gano cewa ta yi amfani da jabun takardun shaidar kammala karatu don samun aiki.

Biyo bayan wadannan bukatu da fafutukar a binciki takardun ma’aikatan ICPC ne hukumar ta kafa wani karamin kwamiti mai mutum uku domin tantance takardun shaidar ma’aikata da bayanan aiki.

An fara aikin tantancewa da aikawa tara daga cikin daraktocin hukumar goma sha daya da suka hada da mataimakan kwamishinoni da kwamishinoni da mataimakan kwamishinoni da kuma daraktoci, wasikar bayyana a gaban karamin kwamitin da aka kafa inda aka bukaci su fito da takardun shaidarsu da bayanan aikinsu domin tantancewa.

Wata majiya hukumar da ta bukaci a sakaya suna, ta ce sakamakon binciken da hukumar ta gudanar ya gano cewa dukkan daraktocin, ban da guda biyu, suna da sabani a bayanansu na takardun shaidar karatu.

A yayin da hukumar ke ci gaba da aikin tantancewar ga manyan ma’aikatan, an ruwaito cewa kwamitin tantancewar ya fitar da wata takarda da ta bukaci matsakaita da kananan ma'aikata 42 wadanda suke kan matakin aiki na 12, 13, da kuma 14, da su bayyana a gabansu ranar 26 ga watan Oktoba.

Majiyoyi daga hukumar sun ce sakamakon aikin tantancewar da aka yi wanda ya bayyana sabanin da aka samu da takardun shaidar kammala karatun ma’aikatan ya sa shugaban hukumar Farfesa Bolaji Owasanoye mai mukamin SAN ya kira babban taro da daukacin ma’aikata da hukumar a ranar 22 ga watan Oktoba, 2021, lamarin da ya sa aka nemi mafita don kubutar da ma’aikatan da abin ya shafa daga yiwuwar korar su daga aiki.

Rahotanni sun yi nuni da cewa hukumar ta bullo ne da hanyar rufawa ma’aikatanta asiri don kare su daga kora da kuma gurfanar da su a gaban kotu bisa la’akari da ka’idojin aikin gwamnati.

Ana zargin cewa hukumar ta yi rufa-rufar ne domin galibin ma’aikatan da abin ya shafa, musamman ma manyan masu biyayya ga shugaban ICPC din ne, da kuma wadanda aka dauka aiki karkashin kulawarsa.

Kokarin ji ta bakin hukumar a yayin hada wannan labari bai sami nasara ba.

XS
SM
MD
LG