Mutane akalla 17 sun mutu yayin da wasu kuma 36 su ka ji raunuka, bayan da wata karamar motar bus (mai dauke da bakin haure) ta yi karo da falwayar wutar lantarki a gabashin kasar Turkiyya, inda ta kama da wuta, a cewar kafafen labaran kasar a yau dinnan Jumma’a.
Direban motar na daga cikin wadanda su ka mutu din, a cewar hukumomin Turkiyya, sannan wadanda su ka ji raunukan, wasunsu ma cikin mawuyacin hali, an kai su asibitin jahar Igdir.
Gwamnan jahar ta Igdir, Enver Unlu, ya ce wasu daga cikin wadandan abin ya rutsa da su sun mutu yayin hadarin, amma wasunsu sun mutu ne lokacin da wata karamar motar bus, wadda ita ma ke dauke da bakin haure, ta markade su.
Kamfanin Dillancin Labaran Gwamnati na Anadolu y ace moyar da ta yi hadatsarin na daren jiya Alhamis akan babbar hanyar Igdir zuwa Kars, na dauke ne da ‘yan kasashen Afghanistan da Pakistan da Iran, wadanda su ka shiga cikin kasar ta Turkiyya ba bisa ka’ida ba, ta kan iyakar Iran.
Karamar motar bus din mai daukar mutane 14, na makare ne da mutane sama da 50, ciki har da mata cewar kafar labaran.
Babban lauyan gwamnati ya fara bincike kan wannan hatsarin, a yayin da kuma jami’ai ke kokarin gano asalin direban.
Facebook Forum