Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bakin Haure 64 Sun Mutu a Tekun Libya


Bakin Haure a Tekun Libya
Bakin Haure a Tekun Libya

Bakin haure kimanin 64 ne ake kyautata zaton sun rasa rayukansu lokacin da masu aikin ceto suka gano wani jirgin da aka shake da mutane, da ya nutse a gabar tekun Libya, a cewar jami’ar jiya Litinin.

Dogarawan teku sun ceto mutane 86 cikin kusan mutane 150 dake cikin jirgin a tekun Meditaraniya ranar Asabar. An gano gawarwaki takwas, dukkansu na mata, ya zuwa yanzu.

Kungiyar kula da bakin haure ta duniya ta kira tekun Meditaraniya a matsayin waje mafi hatsari a duniya, bayan da bakin haure 2,832 suka hallaka a shekarar 2017, haka kuma a shekarar 2016 bakin haure 4,581 dake kokarin zuwa Italiya daga Arewacin Afirka suka rasa rayukansu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG