Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bakin Haure 83 Daga Nahiyar Afirka Sun Mutu a Teku


Bakin haure 83 daga nahiyar Afirka sun mutu, wasu uku sun tsira da ransu lokacin da jirgin ruwansu ya nutse kwanaki biyu da suka gabata, a gabar tekun Tunisia, a cewar dogarawan teku.

Jirgin ya nutse ne a tekun Meditaraniya kwanaki biyu da suka gabata, ‘yan sa’o’i bayan da suka taso daga garin Zuwara na kasar Libya.

Wani masunci ne ya gano mutane hudu kan wasu katakai akan ruwa, ya kuma shaida wa hukumomi. ‘daya daga cikin mutane hudun da suka tsira daga bisani ya rasu a asibiti. Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce jirgin yana dauke da mutane masu yawan gaske ne.

‘Daya daga cikin wadanda suka tsira ya ce ruwa ne ya fara cin jirgin yayin da bakin hauren suke iya ganin haske a bakin gabar ruwa. Kiran waya na gaggawa domin neman taimako bai sami nasara ba, saboda wanda ya kira ya kasa fadawa ma’aikatan ceto inda jirgin nasu ya ke.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG