Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bakin Hauren Da Ke Texas Na Cikin Mawuyacin Hali - Rahoto


Wani sabon rahoto da Sipeta Janar na hukumar tsaron cikin gida ta Amurka wato (Homeland Security) ya fitar, ya kwatanta yanayin cunkoson da ke cibiyar da ake tsare da bakin haure a jihar Texas, a matsayin mummunan yanayi, inda har wani babban jami’in cibiyar ya ce yana yi wa ma’aikatansa fargaba, domin a kowanne lokaci lamarin zai iya rincabe wa.

Rahoton wanda aka fitar da shi a jiya Talata, ya hada har da hotunan mutane tsare a cikin keji suna kwance a kasa, ba tare da suna wani abu ba.

Sannan hotunan sun nuna yadda wasu mutane a wani daki suke tsaye, da wasu maza da mata daban sanye da abin rufe fuska, suna sauraren masu daukan hoton.

Wani hoto na daban, ya nuna wasu mutum 88 da aka cusa a wani daki da aka gina domin zaman mutum 40, inda har daya daga cikinsu ya rike wani kwali da aka rubuta “a taimake mu.”

Rahoton ya bayyana cewa, wasu daga cikin bakin hauren sukan cusa safa a cikin ramin ban dakin da aka ajiye su, domin ya cushe a kira mai gyara don kawai su samu damar fita waje.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG