Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

BAL: Kungiyar Petro Ta Angola Ta Kai Zagayen Quarter-Final


Karawar Petro de Luanda da FAP ta kasar Kamaru
Karawar Petro de Luanda da FAP ta kasar Kamaru

‘Yan wasan na Angola sun kai zagayen ne bayan da suka doke FAP na kasar Kamaru da ci 66-64.

‘Yan wasan Petro de Luanda na kasar Angola sun zama na biyu a shiga zagayen wadanda za su kara a quarter-finals a gasar cin kofin zakarun kwallon kwando ta nahiyar Afirka ta BAL da ake yi a Kigali, Rwanda.

Masu masaukin baki Patriots of Rwanda, su suka fara zuwa zagayen na quarter-finals a ranar Laraba.

‘Yan wasan na Angola sun kai zagayen ne bayan da suka doke FAP na kasar Kamaru da ci 66-64.

A wasansu na farko sun doke ‘yan wasan AS Police Mali da ci 84-66.

Gasar ta BAL ta shiga kwana na biyar kenan a ranar Alhamis, inda kungiyoyi 12 ke neman lashe kofin wannan gasa wacce ake yin ta a karon farko.

An kirkiri wannan gasa ce da hadin gwiwar hukumar kwallon Kwandon Amurka ta NBA da kuma ta kwallon Kwando ta duniya.

Kungiyoyi 12 daga nahiyar Afirka suka shiga wannan gasa, wadanda suka hada da, Algeria, Angola, Kamaru, Masar.

Sauran kasashen sun hada da Madagascar, Mali, Morocco, Mozambique, Najeriya, Rwanda, Senegal da kuma Tunisia.

Wannan shi ne karon farko da hukumar NBA ta kaddamar da wata gasa a wajen yankin arewacin Amurka. Ga jerin sunayen kungiyoyin da zakarun ‘yan wasansu da suka fi fice.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG