Ilelah wanda kwararre ne a fannin watsa labarai, zai maye gurbin Farfesa Armstrong Idachaba.
Ministan yada labarai, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana sauyin cikin wata sanarwa da mataimakinsa na musamman Segun Adeyemi ya fitar a ranar Juma'a.
“Ilelah zai yi shekara biyar a wa’adinsa na farko.” Sanarwar ta ce.
Wannan sauyi da gwamnatin Najeriya ta yi, na zuwa ne yayin da kasar ke takaddama da kamfanin Twitter, wanda aka haramta amfani da shi a kasar.
A farkon makon da ya gabata hukumar ta NBC ta ba kafafen yada labarai na talabajin da rediyo umarnin su rufe shafukansu na Twitter.
Umarnin ya biyo bayan rufe kafar Twitter da aka yi a Najeriyar a ranar Juma’ar da ta gabata, matakin da ya fara aiki a ranar Asabar.
Hukumomin Najeriya, na shirin tilasta wa duk kafafen sada zumunta, yin rijista a kasar kafin a bar su ci gaba da aiki.
Matakin katse kafar sada zumuntar na shan suka a ciki da wajen Najeriya, wacce ta ce ana amfani da shafin wajen ta da zaune tsaye.
A makon da ya gabata Twitter ya goge wani sako da shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa, wanda ya ce ya saba ka’idar kamfanin, dalilin da ake ganin ya sa Najeriya ta haramta amfani da Twitter.