Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

BALTIMORE: Bayan Gagarumin Maci Yanzu Ana Zaman Zullumi


Kwamishanan 'yansandan Baltimore Anthony Batts yana bayyanawa jama'a cewa sun mika sakamakon bincikensu da ma'aikatar shari'r jihar Maryland

Bayan gagarumin macin ranar Alhamis yanzu an samu sakamakon binciken da 'yansanda suka gudanar amma sun ki su bayyanawa jama'a lamarin da ya sa ana zaman zullumi a birnin Baltimore

Jiya Alhamis ne masu zanga zanga a birnin Baltimore suka gudanar da wani gagarumin maci kan titunan birnin, yayinda ake kara samun rade rade dangane da sakamakon binciken da ‘Yansanda suka gudanar gameda mutuwar Freddie Gray.

Matashin ‘dan shekaru 25 da haihuwa, ya mutu ne sanadiyar raunin da ya ji a bayansa ranar 19 ga watan Afirilu yayinda yake hannun ‘yan sanda.

Mutuwar sa ta janyo zanga zanga masu yawa a unguwannin bakaken fata a birnin Baltimore.

‘Yan sanda sun tura rahoton binciken da suka gudanar zuwa ga ofishin babban lauyan gwamnatin jihar, inda za’a yanke shawarar ko za’a tuhumi ‘yan sanda shida ‘din da suka kame matashin.

Kusan komi ya lafa a birnin tun bayan tarzomar da aka yi ranar Litinin. Duk da haka ‘yansanda suna shirin fuskantar karin zanga zanga idan aka bayyana rahoton binciken da suka gudanar. Jami’an ‘yan sanda dai sunki su bayyana abin da suka samo a binciken.

Ko a daren jiya Alhamis ma, masu zanga zangar kan cin zarafin da ‘yan sanda ke yi, sunyi maci a birnin na Baltimore. Haka nan an yi maci ma a garuruwan da suka hada da Cincinati da Philadephia, inda ‘yan sanda suka hana masu zanga zangar rufe manyan tituna.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG