Accessibility links

Ana cigaba da samun tashin bama bamai a kasar Afghanistan inda jiya ma wani ya tashi a kudancin kasar ya yi sanadiyar mutuwara akalla mutane goma

Wani bam da aka boye a gefen hanya, ya tashi ya kashe akalla mutane goma sha uku a kudancin kasar Afghanistan.

Jami'an yankin sunce tashin bam din ya apkawa wata motar dake jigilar farar hula a yayinda suke tafiya akan wata hanyar da babu kwalta a gundumar Maiwand na lardin Kandahar.

Jami'ai sunce an karkata akalar motoci su bi wannan hanya daga babar hanya, bayan tashin wani bam na dabam daya auna sojojin kasashen waje.

Bam din ya tashi kwanaki biyu, bayan yan kasar sun jefa kuri'a zaben shugaban kasa da wakilan Majalisun kananan hukumomi.

Dama kuwa kungiyar Taliban tayi barazanar sa kafar angulu ga zaben, to amma duk da wannan barazana, anyi zaben bayan anyi makoni ana kai hare haren da suka auna 'yan siyasa da yan jarida da kuma jami'an tsaro.
XS
SM
MD
LG